Isa ga babban shafi
Iraqi

Mabiya Shi'a sun yi gangamin jimamin kisan jikokin Annabi

Daruruwan mabiya Shi’a sun gudanar gangami a birnin Karbala na Iraqi kamar yadda suka saba duk shekara domin gudanar da ibada ta jimamin kisan jikokin Manzon Allah (S.A.W).

Mabiya Shi'a na nuna bakin cikinsu da kisan jikokin Annabi a Karbala
Mabiya Shi'a na nuna bakin cikinsu da kisan jikokin Annabi a Karbala REUTERS/Amit Dave
Talla

Mabiyan daga Iraqi da Iran sun gudanar da bikin na Ashura tare da bayyana adawa da kuri’ar da kurdawa suka kada ta ballewa daga Iraqi.

A gangamin, Mabiyan na Shi’a na yin kukan makoki tare da buga kirji a bikin na Ashura, wasu ma na yanka kansu da wuka ko takobi jini ya yi ta tsiyaya domin nuna bakin ciki.

Duk shekara dai, mabiya Shi’a musamman daga Iran da Iraqi na kai ziyara hubbaren Imamu Hussian a Karbala da ke da nisan kilomita 80 da Bagadaza na Iraqi.

Sai dai a yayin bikin, mabiyan sun ta yayata kalamai na yin allawadai da shugaban Kurdawa, Massud Barzani suna cewa shi ne jagoran taba Iraqi.

A ranar 25 ga watan jiya na Satumba, Kurdawa suka jefa kuri'ar raba gardama domin ballewa daga Iraqi, duk da adawar da suka fuskanta daga Iraqi da Iran da Turkiya da kuma kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.