Isa ga babban shafi
Amurka

Dan bindiga ya kashe mutane 50 a gidan rawa na Las Vegas

Akalla mutane 50 sun rasa rayukansu yayin da sama da 200 suka jikkata bayan wani mutun dauke da bindiga ya bude wuta a wani gidan rawa da ke birnin Las Vegas na Amurka.

Mutane 20 sun mutu a harin Las Vegas na Amurka
Mutane 20 sun mutu a harin Las Vegas na Amurka David Becker/Getty Images/AFP
Talla

Wani Jami’in ‘yan sanda a birnin, Joseph Lombardo ya shaida wa taron manema labarai cewa, suna da alkaluman mutane sama da 100 da lamarin ya shafa.

A cewar Lombardo, an yi nasarar kashe maharin bayan musayar wuta da jami’an ‘yan sanda.

Dan bindigan ya fara bude wutar ne tun daga hawa na 32 na Otel din Madalay Bay da ke kusa da gidan rawar.

Hotunan bidiyon da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna yadda aka dauki tsawon lokaci ana jin karar harbin bindiga, lamarin da ya tarwatsa taron jama'a da ke shagali a gidan rawar.

Tun daga ranar Jumma’ar da ta gabata ne aka fara bikin kade-kade da raye-raye a Otel Otel da ke zirin Las Vegas, amma  a yanzu an rufe Otel da dama saboda aukuwar wannan harin.

‘Yan sanda sun ce, a halin yanzu suna neman wani mutum da aka bayyana a matsayin abokin tafiyar maharin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.