Isa ga babban shafi
KOREA TA AREWA

Shugaba Kim Jong-UN ya diga ayar tambaya kan lafiyar Trump

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-Un ya bayyana shugaba Donald Trump a matsayin mai fama da tabin hankali, inda ya sha alwashin mayar da martini kan barazanar murkushe kasarshi da shugabn ya yi.

Kim Jong-Um
Kim Jong-Um KCNA via REUTERS
Talla

Shugaba Kim ya ce zai tabbatar da shugaban na Amurka ya ji a jikinsa kan barazanar da ya yi wa Koriya, inda kuma ya yi tambaya kan halin lafiyar shugaba Trump kan barazanar da ya furta a cikin zauren Majalisar Dinkin Duniya.

Shugaba na Koriya ya ce bisa al’ada, karen da ya razana shi ya fi kowanne haushi, saboda haka yana bai wa Trump shawara ya dinga zaben kalmominsa lokacin da ya ke jawabi a bainar jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.