Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Shugabannin kasashe 130 sun hallara a taron Majalisar Dinkin Duniya

A yau Talata aka fara taron shugabannin kasashe a zauren majalisar dinkin duniya da ke New York, wanda a karon farko shugaban Amurka Donald Trump zai bayyana gabansa. Abinda zai fi daukar hankula a taron na yau shi ne batun makamin nukiliyar Korea ta Arewa, Iran da kuma halin da Musulmi ‘yan kabilar Rohingya ke ciki.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. Reuters
Talla

Akalla shugabannin kasashen duniya 130 ne ke halartar taron na yau, wanda idanunsu ke kan Donald Trump wanda manufarsa ta fifita Amurka fiye da komai ke razana kawaye da kuma abokan hamayyar kasar.

Kafin zuwan wannan lokacin dai Amurka wadda ke kan gaba wajen bai wa majalisar dinkin duniya gudunmawar kudade, ta yi barazanar zaftare kaso mai yawa daga ciki, matakin da sakataren Majalisar Antonio Gutterres ya ce ba shakka zai haifar da gagarumar matsala muddin ya tabbata.

Ana sa ran ministocin harkojin wajen kasashen duniya su tattauna batun tilasta aiwatar da sabbin takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakabawa Korea ta Arewa sakamakon gwajin makamin nukiliyar da ta yi a baya-bayannan.

Dangane da batun kisan ‘yan kabilar Rohingya kuwa sakataren harkokin wajen Birtaniya Boris Johnson ne zai jagoranci taro tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen duniya da kuma jakadan kasar Myanmar kan kisan da MDD ta ce na kare dangi ne akewa Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.