Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Kasashe 60 sun bukaci a haramta sayar da wasu nau'ikan makamai

Wasu kasashen duniya 60 bisa jagorancin kungiyar Tarayyar Turai sun kaddamar da wani yunkuri domin tilastawa MDD haramta cinikin wasu kananan makamai da ake amfani da su domin azabtarwa ko kashe jama’a.

kimanin kasashe 60 ne dai ke bukatar MDD ta samar da dokar haramta sayar da nau'ikan kananan makaman da ake amfani da su wajen halaka jama'a cikin sauri.
kimanin kasashe 60 ne dai ke bukatar MDD ta samar da dokar haramta sayar da nau'ikan kananan makaman da ake amfani da su wajen halaka jama'a cikin sauri. Reuters
Talla

Cikin kasashen da masu wannan fafutuka ke harara akwai kasar Amurka inda har yanzu su ke aiwatar da kisa, da kasar China da Iran da Saudiya wadanda aka ce su ne sahun gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa.

Kasar Amurka musamman na shan suka saboda amfani da naurorin wutan lantarki wajen kashe mutane, kamar dai yadda Gidauniyar Omega Research Foundation ke cewa.

Kasar Argentina da Mongolia sun bi sahun tarayyar Turai wajen wannan fafutuka ta hana amfani da wasu na'urori domin kisan mutane.

Bayanai daga New York inda ake gudanar da babban taron MDD na cewa kasashen Canada, Mexico da wasu kasashen latin Amurka da yawa zasu rattaba hannu cikin wannan yarjejeniya da ake shirin gabatarwa.

Tun a shekara ta 2005 Kungiyar Tarayyar Turai ta dauki matakin haramta azabtar da mutane a kasashen kungiyar 27, har ma ta mai da shi ginshiki cikin manyan manufofinta na waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.