Za a kara samar da tudun muntsira a Syria karo na 4
Kasashen Rasha da Iran da Turkiya sun amince su sake samar da tudun muntsira a Yankin Idlib wanda shine na 4 a Syria, a kokarin da Moscow wacce ke jagorancin zaman ke yi wajen ganin ta kawo karshan yakin basasan kasar.
Wallafawa ranar:
A wata sanarwar hadin-gwiwa da suka fitar bayan taron kwananki 2 a Kazakhstan, kasashen 3 sun cim-ma matsayar tura dakarunsu yankin Idlib da ‘yan tawaye ke rike da shi domin bada kariya da wasu yankunan makwabta da suka hada da Latakia da Hama da Aleppo.
Tattaunawar da akayi a birnin Astana na Kazakhstan shine na 6 da Rasha ke jagoranta a cikin wannan shekarar a kokarin da ta ke wajen kawo karshan zub da jinni a kasar da yakin shekaru 6 ya tagayara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu