Isa ga babban shafi
Iran

IAEA ta mayar da martani kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Hukumar da ke kula da samar da makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, IAEA, ta mayar da martani kan caccakar da Amurka ta yi mata dangane da yarjejeniyar Nukiliyar Iran.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani MOHAMMAD BERNO / IRANIAN PRESIDENCY / AFP
Talla

Hukumar ta hakikance cewa, ta gudanar da zurfafan bincike kan batun Nukiliyar Iran, inda ta ce, ta gano Iran na mutunta yarjejeniyar da ta kulla da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Shugaban Amurka Donlad Trump na ta kokarin samu Iran da laifi kin mutunta yarjejeniyar, domin aiwatar da manufarsa a kanta, a kokarin da ya ke wajen sake kakabamata jerin takunkuman karayar tattalin ariziki da yarjejeniyar ta nukiliyar ta dage wa kasar.

Shirin Nukliyar da aka cim-ma tsakanin Iran da manyan kasashen duniya an sha kai ruwa rana kafin cim-ma yarjejeniyar da ta haifar da mayar da wukakai kube tsakanin Iran da kasashen masu kujerun din-din-din a kwamitin tsaro na MDD

To amma sabon shugaban Amurka da ya gaji yarjejeniyar daga magabacinsa Barack Obama tun lokacin yakin neman zabensa ya sha alwashin kawo karshenta, matakin da ya hadu da suka daga sauran kasashen da suka amince da ita

Shugaban hukumar samar da makamashin Nukliyar IAEA, Yukiya Amano, ya ce zuzurfan binciken da suka gudanar ya tabbatar masu da cewa 'Iran na mutunta yarjejeniyar ta 2015 tare da karyata zargin da Amruka ke yi cewa Iran bata mutunta ta ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.