Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Dalilan da ke jefa matasa shiga ayyukan ta'addanci

Majalisar Dinkin Duniya ta ce talauci da kuma yadda jami’an tsaro ke cin zarafin matasa ke sanya mafi yawansu shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda amma ba tsatsauran ra’ayin addini ba.

Tambari hukumar raya kasashe ta Mdd.
Tambari hukumar raya kasashe ta Mdd. UN
Talla

Hukumar kula da ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniyar ta ce bayan tambayoyin da ta yi wa wasu matasa 600, ta gano cewar abu ne mai sauki ga kungiyoyi irin su Al Shebaab da Boko Haram su dibi matasan da ba su da aikin yi ko kuma wadanda suke fushi kan yadda gwamnati ta gaza wajen samar musu da ayyukan yi.

Kashi 70 cikin dari na matasan da aka yi wa tambayoyin sun bayyana cewar kamawa ko kuma kashe wani nasu da jami’an tsaro suka yi ko kuma wani rashin adalci da aka yi mu su ne ya sanya su shiga irin wadanann kungiyoyi.

Rahotan binciken ya nuna sabanin cewar rashin ilimin addini mai zurfi da ake cewa shi ne ke sanya matasa shiga irin wadannan kungiyoyi, inda yake cewa fahimtar ilimin addini na kauda mutane daga shiga ayyukan ta’addanci.

An dai gudanar da wannan bincike ne a kasashe 6 ciki har da Kenya, Najeriya da kuma Somalia.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.