Isa ga babban shafi
Amurka

Akwai nau'in roba a ruwan da mutane ke sha- bincike

Masana kimiyar lafiya sun ce ruwan famfo da ake na dauke da kananan robobi tsakanin 3,000 zuwa 4,000 da mutane ke sha a ciki a kowacce shekara ba tare da sun sani ba.

Mutane na shan robobi a cikin ruwan da suke sha  tsakanin 3,000 zuwa 4,000 duk shekara
Mutane na shan robobi a cikin ruwan da suke sha tsakanin 3,000 zuwa 4,000 duk shekara Wikipedia
Talla

Masanan sun ce duk da ya ke mutane ba su da masaniya game da illar ruwan da suke sha, binciken ya nuna cewar da na’urar bincike kawai ake iya ganin robobin da ke dauke da sinadari mai guba da ke iya yi wa jama’a illa.

Masana kimiyan daga Jami’ar New York da Jami’ar Minnesota sun bayyana cewar sun gudanar da binciken ne a kasashe 14 na duniya, inda suka dibi ruwan famfo 159 kuma sakamakon binciken ya nuna cewar kashi 83 na ruwan da aka yi gwaji na dauke da sinadarin robar.

Masanan sun ce yayin da aka dauki dogon lokaci ana gudanar da bincike kan illar da robobi ke yi a koguna da tafkuna da bakin teku da kuma muhalli, akasarin bincike bai mayar da hankali kan robar da mutane ke dirka a ciki ba.

Masanan sun ce wannan shi ne bincike na farko da aka yi akan ruwan sha, kuma cikin kasashen da aka gwada ruwan su sun hada da Uganda da India da Indonesia da Lebanon da Amurka da wasu kasashen Turai.

Masanan sun ce cikin kowace lita guda akwai kashi sama da 4 na irin wannan sinadarin roba da mutane ke sha, kuma matsalar ta fi girma ne a kasashen da ke Arewacin Amurka da kuma wasu kasashen Turai guda 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.