Goguwar Irma ta doshi Amurka
Hukumomin Jihar Florida da ke Amurka na shirin fuskantar wata guguwa mai dauke da ruwan sama da aka yi wa lakabi da Irma wanda ke tafiyar kilomita 295 a cikin awa guda da ta doshi Yankin.
Wallafawa ranar:
Tuni aka bukaci bakin da ke Jihar da su fice yau laraba, yayin da mazauna Yankin za su bi sawunsu daga baya kafin rufe tashar jiragen sama.
Masana Yanayi sun bayyana guguwar Irma wadda yanzu haka ta dumfari Yankin Carribean da Jihar California da su nemi mafaka saboda hatsarin da ke tattare da ita.
Ana sa ran guguwar ta afkawa tsibiran da ake yawon bude ido da ke Saint Martin da Saint Barthelemy da kuma Jihar California da ke Amurka.
Guguwar na tafiyar kilomita 360 a cikin awa guda, yayin da ake sa ran rufe tashoshin jiragen sama a California.
Tuni shugaba Donald Trump ya kafa dokar ta baci a Jihar ta Florida, kamar yadda aka yi a Puerto Rico da kuma wasu tsibiran da ke Yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu