Isa ga babban shafi
Australia

Australia zata gudanar da kuri’ar jin ra’ayi kan auren jinsi

Australia na daya daga cikin kasashen da har yanzu basu amince da auren jinsi guda ba, duk da bukatar wasu 'yan kasar.Yanzu haka gwamnatin kasar na shirin gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a domin ganin sun bayyana ra’ayin su akai.

Auren jinsu guda na samu karbuwa a wasu kasashen Duniya
Auren jinsu guda na samu karbuwa a wasu kasashen Duniya AFP PHOTO / KENZO TRIBOUILLARD
Talla

A watan gobe ne ake saran bai wa ‘yan kasar Australia damar bayyana ra’ayoyin su kan bukatar da wasu ke da ita na auran jinsi guda, wanda hakan zai bai wa Majalisar kasar damar fara mahawara a kai a cikin wannan shekara.

Ya zuwa yanzu dai kasashen duniya 24 suka amince da auren, wadanda suka hada da Argentina da Belguim da Brazil da Birtaniya da kuma Canada.

Sauran sun hada da Colombia da Denmark da Faransa da Findland da Greenland da Jamus da Iceland da Luxembourg da Malta da Mexico da Netherlands.

Sai kuma New Zealand da Portugal da Afirka ta kudu da Spain da Sweden da Uruguay da Amurka.

Kasar Netherlands ce ta farko da ta amince da auran a duniya, yayin da Afirka ta kudu ta zama ta farko daga Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.