Isa ga babban shafi
Fasaha

Kwararru sun gargadi kera sakandamai a duniya

Masana kimiyya da suka kware kan fasahar kera mutun-mutumi da wasu suka fi sani da sakandami, sun bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta haramta kera sakandaman da za a iya amfani da su wajen kisan jama’a da kuma a fagen yaki.

Masana kimiyya sun ce kera sakandamai don yaki na da matukar hadari a duniya
Masana kimiyya sun ce kera sakandamai don yaki na da matukar hadari a duniya REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Cikin wasikar da suka aikewa Majalisar, sama da masa kimiyya 100 sun yi gargadin cewa, bunkasa fasahar za ta iya haddasa zubar da jini mai yawan gaske.

Masanan dai sun yi gargadin cewa fasahar kera Sakandaman ba tare da sa idon kowace hukuma ba, wadda a kimiyyance ake kira da Pandorra tana da matukar hadarin gaske, kasancewar zai bada damar amfani da su wajen gwabza yake- yaken da dan Adam ba zai iya kiyasta muninsu ba.

A dalilin haka ne kwararrun bisa fasahar ta kere-kere 116 suka rattaba hannu kan takardar da ke bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta haramta damar da a wasu kamfanoni ke da ita ta kera ire-iren sakandaman masu siffar dan Adam ba tare da neman izini ba.

A cewar masanan, daga cikin hadarin da ake fuskanta, shi ne yadda kungiyoyin ‘yan ta’adda ka iya amfani da damar wajen yi wa jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba kisan kiyashi idan har sakandaman suka fada hannunsu, ko kuma suka yi amfani da ilimin na’ura mai kwakwalwa wajen sauya ainihin bayanan da aka dura cikin kwakwalwar sakandaman

A cewar masana kimiyyar, tilas ne Majalisar Dinkin Duniya ta shigar da kera mutun-mutumi cikin jerin makaman da ta haramta kerawa kamar yadda kwararru kan fasahar kere-kere 1000 suka bukata a shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.