Kim Jong Un ya jikirta kai hari tsibirin Guam
Kasashen China da Rasha sun bukaci gudanar da tattaunawa domin rage tankiyar da ake samu tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa bayan da shugaba Kim Jong-Un ya jinkirta kai harin tsibirin Guam.
Wallafawa ranar:
China kasar da tafi kusanta da Koriya ta Arewa tace rikicin Amurka da Koriya ya kai wani matakin dake bada tsoro, saboda haka lokaci yayi da ya kamata a je teburin tattaunawa.
Ma’aikatar harkokin wajen China, ta bakin Hua Chunying, China na fatar gani an cimma daidetuwa da zaman lafiya.
Rahotanni sun ce, ministan harkokin wajen China Wang Yi ya tattauna da takwaran sa na Rasha Sergei Lavrov ta waya, inda suka amince da shirin gudanar da taro domin kawo karshen tankiyar.
Shima Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson yace a shirye suke su tattauna da Koriya ta Arewa muddin ta amince ta aje makaman ta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu