Isa ga babban shafi
Amurka

Bush da dansa sun caccaki kyamar juna a Amurka

Tsoffin shugabannin Amurka George H. W Bush da dansa George W. Bush sun fitar da wata zazzafar sanarwar hadin-gwiwa, in da suka soki zanga-zangar nuna kyama da aka gudanar a Charlottesville na jihar Virginia. Ana kallon wannan sanarwa a matsayin caccaka ga shugaba Donald Trump, wanda aka zarga da daukan bangaranci a zanga-zangar.

Tsohon shugaban Amurka George W. Bush
Tsohon shugaban Amurka George W. Bush REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Shugaba Trump ya rura wutar siyasar Amurka saboda kalamansa na ranar Talata da ke nuna cewa, yana goyon bayan masu zanga-zangar nuna wariyar launin.

A yayin zanga-zangar dai, wata matashiya ta rasa ranta bayan wani matukin mota ya afka kan wasu mutane daban da su kuma ke zanga-zangar adawa da nuna wariyar launin.

Shugaba Trump dai ya sha caccaka saboda yadda ya dauki bangaranci a zanga-zangar, yayin da tsoffin shugabannin kasar biyu, wato George H. W Bush da kuma dansa George Bush suka fitar da wata sanarwar hadin gwiwa daga gidansu na gado da ke Kennebunkport, in da suka ce dole ne, Amurka ta yi watsi da matsalar nuna wariya da kyamatar juna a kowanne lokaci.

Shugannin biyu su bada misali da Thomas Jefferson da ya jagoranci sanar da samun yancin kan kasar wanda kuma ya kasance dan asalin Monticello da ke garin na Charlottesville.

Shugabannin sun ce, suna yi wa Charlottesville addu’a kuma suna tuta gaskiyar da Jefferson ya assasa a matsayinsa na fitaccen dan kasar da ya fito daga yankin.

Sanarwar Bush da Bush ta ce, kowa na da 'yancin gudanar da rayuwarsu kuma an halicce mu ne babu wanda ya fi wani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.