Isa ga babban shafi
Amurka

Chicago ya maka gwamnatin Donald Trump a gaban kotu

Birnin Chicago ya maka gwamnatin Donald Trump a gaban kotu domin kalubalantar matsayin shugaban, na rikewa biranen da suka ki aiwatar da umurnin sa na kama baki marasa takardun zama kudaddensu.

Birnin Chicago ya maka gwamnatin Donald Trump a gaban kotu
Birnin Chicago ya maka gwamnatin Donald Trump a gaban kotu Reuters / Kevin Lamarque / File Photo
Talla

Shari’ar irin ta na farko na kalubalantar matsayin shugaban na neman hadin-kai wajen kama irin wadannan baki domin mayar da su kasashen su ko kuma gwamnatin tarayyar ta ki basu kudaden kula da ‘Yan Sanda.

Magajin Garin Chicago Rahm Emmanuel ya bayyana matakin a matsayin koma baya.

Babban lauyan gwamnatin Amurka Jeff Sessions ya ce ba za su bai wa biranen da suka karya doka kudin gwamnati ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.