Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

An rantsar da Rouhani don fara wa'adi na biyu

An rantsar da shugaba Hassan Rouhani na Iran don fara wa’adi na biyu akan karagar mulki, yayin da a bangare guda ya gargadi Amurka dangane da warware yarjejeniyar Nukilayar da kasarsa ta kulla da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani President.ir/Handout via REUTERS
Talla

Baki daga kasashen ketare na cikin mahalarta bikin rantsar da Rouhani a yau Asabar, da suka hada da shugabar diflomasiyar Kungiyar Tarayyar Turai, Federica Mogherini wadda ta lashi takobin ci gaba da karfafa dangantaka da Iran duk da matsin lambar da kasar ke fuskanta daga Amurka.

Kazalika shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na cikin manyan baki.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, Rouhani ya sake lashe zaben shugabnacin kasar bayan ya doke Ebrahim Raisi mai tsattsauran ra’ayi.

Rouhani ya yi alkawarin ci gaba da hulda da kasashen Yamma tare da samar da tsare-tsare masu sassauci a kasar.

Sai dai shugaban na shan caccaka saboda game da neman hadin kan masu tsattsauran ra’ayi don kafa sabuwar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.