Isa ga babban shafi
Bincfike

Mutane sun karar da rararsu ta ruwa a bana- Rahoto

Wani rahoton bincike ya nuna cewa, daga yau 2 ga watan Agusta al’ummar duniya ke karar da dukkanin rararsu ta albarkatun kasa da suka hada da ruwa da iska mai kyau na wannan shekara ta 2017.

Ana fama da karancin ruwan sha mai tsabta a Afrika
Ana fama da karancin ruwan sha mai tsabta a Afrika AfricAqua
Talla

Rahoton wanda kungiyoyin gwagwamayar kare muhalli na duniya suka fitar ya ce, a wannan rana al’ummar duniya suka cinye rararsu ta albarkatun kasa da ruwa da kuma iska na bana

Abin lura anan shi ne, mutanen duniya sun yi gaggawar cinye rararsu ta 2017 idan aka kwatanta da bara.

Rahoton ya ce a halin yanzu, mutanen duniya za su fara cin rararsu ta badi a cikin wannan shekara, abin da ya saba wa ka’idojin kimiya, domin duniya na bukatar akalla shekara guda don murmurewa daga abubuwan da aka diba daga cikinta.

Kungiyoyin kare muhallin sun ce, a cikin watanni bakwai, an fitar da hayaki mai gurbata muhalli fiye da kima ta yadda ya zarce karfin tekun da dazukan da ke hadiye hayakin a shekara guda.

Sannan kuma an kama kifaye masu dimbin yawa, baya ga sare itatuwa da kuma girbin da ya wuce kima.

Binciken ya ce mutanen na duniya sun yi amfani da ruwa fiye da adadin da kasa ke iya bayarwa a shakara guda.

An samu irin wannan matsala a ranar 21 ga watan Oktoban shekarar 1993 da ranar 22 ga watan Satumban shekarar 2003, da kuma ranar 13 ga watan Agustan shekarar 2015.

Rahoton y ace mutane na iya taimakawa wajen kawo karshen matsalar ta hanyar takaita cin nama da rage zubar da abinci da kuma rage kone makamshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.