Amurka na atisayen soji don razana Koriya ta Arewa
Kasashen Amurka da Koriya Ta Kudu na gudanar da atisayen soji da ya kunshi harba makamai masu linzami daga wannan sashi zuwa wancan don razana Koriya ta Arewa da ta yi sabon gwajin makami mai linzami.
Wallafawa ranar:
Sai dai Koriya ta Arewa ta yaba da nasarar da ta samu a sabon gwajin mai cin dogon zango, abin da ta ce, gargadi ne ga Amurka.
Shugaban kasar, Kim Jong-un ya ce, gwajin na baya-bayan nan ya nuna cewa, dukkanin Amurka na cikin da’irar da hari zai shafa
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gwajin a matsayin hatsari, yayin da China ta soki matakin, in da kuma ta bukaci bangarorin biyu da su kai zuciya nesa.
Faransa ta bukaci mambobin kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da su gaggauta kara kakaba wa Koriya Ta Arewa takunkumi bisa gwajin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu