Isa ga babban shafi
Amurka

Majalisar dattawan Amurka ta ki soke dokar Obamacare

Yunkurin soke shirin inshoran lafiyar Obamacare ya sake samun koma baya a Majalisar Dattawan Amurka, inda ‘yan Majalisu 51 suka ki amincewa da shirin, yayin da 49 suka goyi bayansa.

Wasu 'yan majalisar Amurka na gudanar da zaman kan inshorar lafiyar Obamacare
Wasu 'yan majalisar Amurka na gudanar da zaman kan inshorar lafiyar Obamacare Somodevilla/Getty Images/AFP
Talla

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Mitch McConnell, ya bayyana takaicinsa dangane da sakamakon kuri’ar, ganin yadda ‘yan Majalisar uku suka bijire wa jam’iyyar tasu wajen kada kuri’ar kin amincewa da shirin.

Cikin wadanda suka kada kuri’ar kin amincewa daga Jam’iyyar Republican sun hada da Sanata John McCain da Susan Collins da Lisa Murkowski.

Wanann ba karamar koma baya ba ce ga shugaba Donald Trump wanda ya tsaya tsayin daka domin ganin an soke tsarin da ke bai wa Amurka kusan milyan 20 dama samun kulawar kiwon lafiya a matsayin kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.