Isa ga babban shafi
IMF-Amurka

IMF ta soke bada lamunin kudi ga kasashe

Asusun bada Lamuni na Duniya IMF zai kaddamar da wani sabon shirin taimakawa kasashen da ke bukatar agaji wanda bai shafi taimaka musu da kudade ba.Asusun ya ce maimakon bai wa gwamnatocin kudade a matsayin tallafi, sabon shirin zai mayar da hankali wajen toshe hanyoyin zurarewar kudaden gwamnatoci ta hanyar bada shawarwari.

Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde
Shugabar Asusun bada lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde Reuters
Talla

Sabon shirin ya shafi lalubo sabbin hanyoyin samun kudade ga kasashen.

A cewar IMF sabon tsarin zai zo dai-dai da bukatar da ake da ita a ainihin shirin sa na bada lamuni ga kasashe, inda za a rika bibiyar yadda tsarin ke tafiya duk bayan watanni shida don tabbatar da samun nasara.

Wasu masana tattalin arziki dai na bayyana damuwa kan yadda kasashen da ke karbar lamuni daga Asusun na IMF ke fuskantar kuncin rayuwa sakamakon sharadodin da ya ke gindaya musu.

Sabon tsarin bayar da lamunin ba tare da kudi ba dai ya ci karo da asalin tsarin da asusun ya ginu akan sa, inda ya ke bai wa kasashen da ke bukatar agaji lamunin wasu kudade bayan ya gindaya musu sharudda.

Asusun na IMF ya ce karkashin tsarin zai rika bibiyar harkokin kudin kasashe ta yadda zai rika taimaka musu wajen karbar kudaden haraji ko bayar da Fansho koma harkokin da suka shafi kwadago.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.