Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Trump ya ce Iran na mutunta yarjejeniyar Nukiliyar

Shugaba Donald Trump na Amurka ya janye bukatarsa ta soke yarjejeniyar nukiliyar Iran, in da jami’ansa suka ce, Amurka za ta ci gaba da mutunta ta muddin Iran ba ta karya sharadodin da aka gindaya ma ta ba.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Gwamnatin Trump ta shaida wa Majalisar Dokokin Amurka cewar, bayanan da suke da su na tababtar musu da cewar, Iran na mutunta wannan yarjejeniya da aka kulla a shekarar 2015.

Majalisar Amurka na bukatar wannan bayani ne domin sanin ko za ta kakaba wa Iran sabbin takunkumi ko kuma a’a.

Wannan shi ne karo na biyu da Trump ke tabbatar da mutunta yarjejeniyar da Iran ke yi, sai dai hakan bai hana kasashen biyu karo ba kan manufofinsu a Gabas ta Tsakiya musamman kasashen Syria da Yemen.

Lokacin yakin neman zabe, shugaba Trump ya yi watsi da yarjejeniyar da gwamnatin Barack Obama da kawayenta su ka kulla da Iran, in da ya sha alwashin sake duba ta, abin da ya janyo suka daga sauran kasashen duniya.

Wannan dai ba sabon abu ba ne dangane da shugabancin Donald Trump wanda ya yi suna wajen tufka da warwara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.