Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya fallasa sakwannin Imel dinsa da Rasha

Babban dan shugaban Amurka Donald Trump Junior, ya fallasa jerin sakwannin Imel da ke nuna yadda ya nemi bayanan batanci daga Rasha kan Uwargida Hillary Clinton da zimmar taimaka wa mahaifinsa samun nasara a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a karshen shekarar bara.

Mr. Donald Trump junior, da ga shugaban Amurka, Donald Trump
Mr. Donald Trump junior, da ga shugaban Amurka, Donald Trump © RFI/Anne-Marie Capomaccio
Talla

Mr. Donald Trump Junior, ya tabbatar cewa, ya nemi bayanan batancin ne kan Clinton a yayin yakin neman zaben Amurka.

Wani mai shiga tsakani daga Rasha, ya shaida wa Trump Junior cewa, zai iya samun wasu bayanan batanci kan Uwargida Clinton a matsayin gudun mawar gwamnatin Rasha a zaben na Amurka.

Jim kadan da jin haka, da ga shugaban na Amurka ya ce, yana kaunar samun ire-iren wadannan bayananan kan Clinton, yayin da kuma ya gaggauata shirya ganawa da majiyar da ta yi masa wannan tayin, kamar yadda sakwannin na Imel suka nuna.

Trump Junior dai, ya fallasa sakwannin na imel ne a shafinsda na Twitter, in da daga bisani jaridar The New York Times ta wallafa su baki daya, kuma sun tabbartar cewa, Moscow ce ke da alhakin bada bayanan batanci kan Hilary Clinton da ta sha kayi a zaben na watan Nuwamban bara.

Wannan sabuwar fallasar ta kara rura wutar badakalar kutsen Rasha a zaben na Amurka da zimmar taikamaka wa shugaba Trump samun nasara, lamarin da ake ci gaba da ece-kuce akansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.