Isa ga babban shafi
WHO

Ciwon sanyi ta hanyar Jima’I a yanzu na bijerewa magani- WHO

Hukumar Lafiya ta duniya WHO ta ce akwai bukatar samar da sabon magani da zai yaki ciwon sanyi da ake samu ta hanyar jima’I, saboda yadda cutar ke neman ta gagari magungunan da ake da su yanzu haka.

Ana kwasar kwayoyin cuta ta hanyar tsotsar al'aura da baki tsakanin maza da mata da kuma ta dubura
Ana kwasar kwayoyin cuta ta hanyar tsotsar al'aura da baki tsakanin maza da mata da kuma ta dubura
Talla

Rahoton hukumar da aka fitar a yau Juma’a ya ce kaucewa yin amfani da kororon roba da tsarin jima’I ta hanyar tsotsar al’aura tsakanin maza da mata na kara haifar da kwayoyin cuta da ke da wahalar magancewa.

Rahoton na WHO ya ce kusan mutane miliyan 80 ne ke kamuwa da cutar ciwon sanyin ta hanyar jima’I duk shekara.

Kuma a kullum likitoci na fuskantar kalubale wajen warkar da cutar da ke bijirewa magungunan da ake da su domin magance cutar nan take.

Rahoton ya kuma yi gargadin cewa yanzu yana da wahala a iya magance cutar nan take idan har mutum ya kamu da ciwon sanyi saboda yadda kwayoyin cutar ba su jin magani.

Hukumar WHO ta gudanar da binciken ne a kasashe 77 na duniya, inda aka gano yanzu ciwon na sanyi na bijerewa magungunan yakar cutar.

Rahoton ya ce yawancin kwayoyin cuta da ake samu ta hanyar tsotsar al’aura da baki tsakanin maza da mata da kuma saduwa ta dubura ne ke bijerewa maganin samun waraka.

Hukumar ta ce akwai bukatar yin binike na musamman domin samar da maganin da zai yaki cutar nan take.

Ciwon sanyi dai na bukatar magancewa nan take idan ba haka ba yana haifar da cututuka da dama da suka shafi rashin haihuwa har ma da yin sanadin rayuwar mutum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.