An datse dala miliyan 600 daga kudaden ayyukan dakarun majalisar dinkin duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 14:11
Bayan share tsawon makonni ana tattaunawa tsakanin kasashen da ke taimaka-wa da kudade, domin daukar dawainiyar ayyukar wanzar da zaman lafiya na dakarun majalisar dinkin duniya, an cimma matsaya domin rage kudaden da kimanin dala milyan 600 a shekara. Kasar Amurka ce dai tayi ruwa tayi tsaki ganin cewa lallai sai an rage wadannan kudade saboda a cewar ta, bangaren samar da tsaro zaman lafiya a duniya na lakume makudan kudade. Kasashen Sudan ta Kudu, yankin Darfur, jamhuriyar Congo, da kasashe irin su Mali, da kuma Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, na daga cikin kasashen Afrika dake samun kudade domin daukar dawainiya irin wannan runduna ta wanzar da zaman lafiya a Afrika. Kan haka ne shirin na Ra'ayoyin Masu sauraron ya bakuk damar tofa albarkacin bakinku a kai.