Isa ga babban shafi
Nigeria-Syria

Ana Bukukuwan Karamar Sallah Yau

A yau Lahadi al'ummar musulmi a sassan duniya da dama aka yi bukukuwan Karamar Sallah bayan kammala azumin watan Ramadan jiya Asabar.

Jami'an tsaro suna tantance masu shiga Masallacin Idi a birin Abuja, Najeriya
Jami'an tsaro suna tantance masu shiga Masallacin Idi a birin Abuja, Najeriya RFI
Talla

Tun daren jiya kasashe da dama suka sanar da ajiye azumin bayan da aka ga jinjirin wata.

Shugabannin kasashen duniya na ta aikewa da sakonnin fatan alheri da ganin wannan rana.

Wasu rahotanni daga kasar Syria na cewa Shugaba Bashar Assad da kansa ya jagoranci sallar Idi a wani al'amari da ba'a saba gani ba.

Bayanan na nuna karon farko kenan yayi sallah a wani gari baya ga birnin Damascus  kasancewar yayi sallar Idi  a garin Hama tare da Ministocinsa.

Kafin Sallar idin Shugaba Bashar Assad ya yiwa fursunoni 670 afuwa albarkacin  wannan Sallah.

Majiyoyi na cewa tun Sallar Idi bara babu wanda ya sake tozali da shi sai yau a filin Idi.

Shima Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aike da sakon fatan alheri da muryarsa inda yayi fatan dorewar zaman lafiya da barin surutai marasa kan gado

A kasar Janhuriyar Nijar an yi Sallar Idi lami lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.