Kasar Qatar ta Nemi Sulhu da Kasashen Larabawa
Kasar Qatar ta roki kasashen Larabawa makwabtan ta da suka janye hulda da ita da su cire mata dukkan wani takunkumi don komawa kujeran tattaunawa da ita.
Wallafawa ranar:
Wannan roko na zuwa ne bayan da kasar Daular Larabawa ke cewa maida Qatar saniyar ware na iya kai shekaru da yawa a haka.
Ministan Waje na kasar Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani ya bayyana cewa jerin takunkumin da aka malkaya masu ya saba hankali.
Ya ce duniya ta sani cewa suna bukatar zama a yi sulhu amma ba da rana tsaka a malkaya masu takunkumi ba.
A ranar biyar ga wannan wata ne dai Kasar Saudiya da kawayenta, Bahrain, Daular Larabawa da sauransu suka malkayawa Qatar takunkumin karairaya ta saboda zargin tana marawa kungiyoyin ta’addanci baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu