Saurare Saukewa Podcast
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 18/01 06h00 GMT
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/01 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/01 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 18/01 06h17 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 18/01 07h00 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 20/01 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 20/01 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 18/01 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/01 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h06 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 16h30 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 18/01 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 18/01 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 18/01 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 19/01 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 19/01 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 18/01 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

An samu wani magani da ya nuna alamun warkar da cutar Kansa

media Cutar Kansa na barazana a duniya Eric Bouvet / Institu Curie

Wani Binciken masana kiwon lafiya a kasar Amurka ya bayyana cewar gwajin maganin cutar kansa mai suna Larotrectinib ya nuna alamomin magance wasu nau’oin cutar a tsakanin masu fama da ita daga manyan mutane zuwa masu kananan shekaru.

Masana masu binciken sun sanar da samar da maganin ne a wani babban taron cutar kansa da aka kudanar a Amurka.

A taron an bayyana cewa maganin zai taimakawa wajen magance wasu nau’ikan cutar da suka hada da kansar mama da ke barazana ga rayuwar mata.

Binciken ya tabbatar da cewa maganin ya yi aiki ga kashi 76 cikin 100 na masu dauke da nau’in cutar kansa 17, da suka hada da kananan yara da manya.

Sannan kashi 79 daga cikinsu sun rayu a tsawon shekara guda, a yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da maganin da ake fatar zai warkar da cutar Kansa.

An gudanar da gwajin maganin kan mutane 55 masu dauke da cutar kansa da suka kunshi manya 43 yara kanana 12.

Sai dai hukumar da ke kula da ingancin abinci da magunguna a Amurka ba ta bada izini soma amfani da maganin ba.

David Hyman da ya jagoranci binciken ya ce Maganin zai kasance na farko a duniya da zai kawo sauki a rayuwar manya da kananan yara da ke fama da radadin cutar Kansa.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure