Isa ga babban shafi
Ecowas- Morocco

Sarkin Morocco ya soke zuwa taron ECOWAS a Liberia don an gayyaci Netanyahu na Isra'ila

Sarkin kasar Morocco ya ki amsar goron gayyatar da Kungiyar ECOWAS ta aike masa  don ya halarci taron Kungiyar da za'a fara gobe lahadi a kasar Liberia.

Sarki Mohammed na shida na kasar Morocco
Sarki Mohammed na shida na kasar Morocco Reuters
Talla

Sarki Mohammed na shida ya bayyana cewa zai kauracewa taron ne saboda gayyatar da aka yiwa Firaministan  Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Kasar Morocco dai na neman shiga kungiyar ce bayan ta sami shiga kungiyar Tarayyar Africa a watan Janairu da ya gabata, bayan kwashe shekaru 33 ba ta ciki.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.