Faransa- DR Congo
Jami'an Tsaro na Janhuriyar Congo sun kubutar da Bafaranshe da ake garkuwa da shi
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewa wani Bafaranshe da ake garkuwa da shi na tsawon watanni biyu a kasar Jamhuriyar Democradiya ta Congo ya sami kubuta.
Wallafawa ranar:
Talla
Shi wannan bafaranshe na cikin mutane biyar da ka sace daga inda suke hakar ma'adinai tun ranar daya ga watan uku na wannan shekara.
Mutanen biyar sun kasance suna aiki ne a kamfanin Banro na kasar Canada dake hakar maadinai a kasar Janhuriyar Democradiyya ta Congo.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya godewa Hukumomin Janhuriyar Congo saboda kokarin kubutar da Bafaranshen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu