Tattaunawar sulhu da 'yan tawaye ta ci tura a Philippines
Tattaunar zaman lafiya tsakanin Gwamnatin Philippines da ‘yan tawayen kasar ta sake sukurkucewa a yau Asabar, sakamakon wani umarni dake neman mayaka ‘yan tawaye su ci gaba da yaki.
Wallafawa ranar:
Sai dai kuma masu shiga tsakani a sulhun na ganin tattaunawan da ake yi a wani yankin gaban ruwa dake Neitherland, za’a ci gaba duk da cewa an sanar da dage tattaunawan.
Bangarorin biyu sun fara tattaunawan sulhu ne , kwatsam sai jagoran tattaunawan Jesus Dureza ya soki yadda ‘yan tawayen ke bukatar mayakansu da su kai hare-hare saboda Shugaban kasar Rodrigo Duterte ya ayyana dokar soja a wasu sassan kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu