Isa ga babban shafi
Birtaniya

Mutane 22 sun mutu a harin Manchester

Hukumomin Birtaniya sun tabbatar da mutuwar mutane 22 sakamakon wani harin ta'addancin da aka kaddamar a wani wurin cashewa da ke birnin Manchester a cikin daren da ya gabata.

Jami'an 'yan sandan Birtaniya na ci gaba da gudanar da bincike kan harin Manchester
Jami'an 'yan sandan Birtaniya na ci gaba da gudanar da bincike kan harin Manchester REUTERS/Andrew
Talla

Wata sanarwa da jami'an 'yan sanda suka fitar, ta tabbatar da mutuwar maharin da ya kai farmakin bayan ya tada bama-baman da ke jikinsa, yayin da kimanin mutane 59 suka jikkata da suka hada da kananan yara.

Shugaban 'yan Sandan Manchester Ian Hopkins ya ce, maharin ya dana bama-bamansa ne a dai dai lokacin da jama'a ke shirin ficewa daga wurin cashewar wadda fitacciyar mawakiyar Amurka Arian Grande ta jagoanta.

Fashewar da aka samu bayan kammala bikin rawar ta jefa dubban mutanen da suka halarci bikin cikin halin rudani, in da kowa ya yi ta kansa domin ganin ya tsira da ransa.

Jami’an aikin gaggawa tare da 'yan sandan tarwatsa bama-baman sun ruga domin kai dauki ga mutanen da hadarin ya ritsa da su.

Firaministar kasar Theresa May ta yi Allah-Wadai da harin, sannan kuma ta dakatar da yakin neman zaben da ta ke yi don jagorantar Majalisar tsaron kasa.

Ita ma mawakiyar Ariana Grande ta aike da sakon ta’aziya ga wadanda harin ya ritsa da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.