Isa ga babban shafi
Iran

Hassan Rouhani ya sake lashe zaben kasar

Shugaba Hassan Rouhani na Iran ya sake lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar jiya Juma’a da kashi 57 cikin 100 na yawan kuri’un da mutane fiye da miliyan 40 suka kada.Yawan kuri’un da ya samu ba sai an sake shiga zagaye na biyu na zaben ba ganin cewa babban abokin hamayarsa mai tsausauran ra’ayi Ebrahim Raisi ya samu kashi 39 cikin dari.  

Hassan Rouhani Shugaban kasar Iran  wanda ya sake lashe zaben kasar
Hassan Rouhani Shugaban kasar Iran wanda ya sake lashe zaben kasar President.ir/Handout via REUTERS/File Photo
Talla

Rouhani mai matsakaicin ra’ayi ya ce al’ummar Iran sun samu nasara kuma zai yi bakin kokarin sa tsawon shekaru hudu nan gaba wajen cika ma su alkawurran da ya dauka.

Dama dai Rouhani ya kulla yarjejeniya da kasashe masu karfi fada aji a duniya game da shirin kasar na nukiliya wanda hakan zai bashi damar kawo sauye sauye a kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.