Isa ga babban shafi
Amurka

Trump na fuskantar kalubale a Amurka

Badakalar alakar Gwamnatin Amurka da Rasha na sake daukan sabon salo, bayan da aka bankado wasu bayanai da ke tabbatar da cewa Shugaba Donald Trump ya yi kokarin hana hukumar FBI gudanar da bincike kan alakar wasu jami’an gwamnatinsa.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Joshua Roberts
Talla

Wannan na zuwa a yayin da Rasha ta ce za ta bayyana tattaunawar da Trump ya yi da manyan Jami’an gwamnatinta.

‘Yan Jam’iyyar Democrats sun bukaci cikakken bayanai akan zarge-zargen yayin da wasu ‘yan Jam’iyyar a majalisa suka bukaci a tsige Trump.

Akwai batun bai wa Rasha muhimman bayanai Sirri kasar, da kokarin hana James Comey gudanar da bincike kan tsohon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro Michael Flynn, batun da idan ya zama gaskiya zai jefa fadar White House cikin babban rikici.

Wasu bayanai na cewa babu tabbas Trump ya yi katsalandan a sha’ani binciken FBI, kwana guda bayan Flynn ya sanar da murabus.

Dalilan da ya sanya wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawan kasar bukatar a fallasa muryoyin tattaunawar Trump da Comey kafin 24 ga watan Mayu.

Tuni dai Shugaba Putin na Rasha ya bayyana cewa a shirye ya ke ya mika tattaunawar da Lavrov da Trump suka yi ga majalisar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.