Isa ga babban shafi
Venezuela

Venezuela za ta fice kungiyar kasashen Amurka

Kasar Venezuela ta yi barazanar ficewa daga cikin kungiyar kasashen da ke yankin Amurka saboda yadda kasashen ke matsin lamba ga shugaban Nicolas Maduro kan rikicin siyasar kasar.

Ana zanga-zangar kyamar gwamnatin Maduro
Ana zanga-zangar kyamar gwamnatin Maduro ®REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Ministan harkokin wajen Venezuela Delcy Rodriguez ta ce gwamnatinsu za ta kaddamar da shirin shekaru biyu da zai ba ta damar ficewa daga cikin kungiyar da ta kunshi har da Amurka.

Kungiyar dai na bayyana damuwa ne kan halin da Venezuela ke ciki musamman ta fuskantar tattalin arziki da rudanin siyasa.

An shafe watanni ‘yan adawa a Venezuela na zanga-zangar kin jinin gwamnatin Maduro.

Rodriguez ta ce Venezuela yanzu ta daina shiga sha’anin harakokin Kungiyar kasashen Amurka ta OAS.

Sakatare Janar na kungiyar Luis Almagro ya bayyana shugaba Nicolas Maduro a matsayin shugaban kama karya, ganin yadda mutane 28 yanzu haka suka rasa rayukansu a zanga-zanga.

OAS da sauran hukumomin kasashen da dama sun bayyana damuwarsu dangane da rikicin kasar da suka ce Maduro ya yi birus, dalilan da ya sanya mambobin kungiyar ke laluben daukar mataki kan Venezuela

Venezuela ta fuskanci kariyar tattalin arziki irinsa mafi muni da hauhawan farashi, tun bayan faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Shugaba Maduro dai na zargin Amurka da taka rawa wajn jefa kasar cikin matsanin yanayi da ta shiga a fannin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.