Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta tsugunar da 'yan gudun hijira 1,200

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya bayyana cewa, kasar za ta mutunta yarjejeniyar da ta cimma da Australia a bara don tsugunar da ‘yan gudun hijira dubu 1 da 250 a Amurka.

Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence 路透社
Talla

Mr. Pence ya shaida wa taron manema labarai a birnin Sydney da ya samu halartar Firaministan Australia Malcolm Turnbull cewa, Amurka za ta yi nazari kan yarjejeniyar wadda ya ce, ko da sun yi aiki da ita, hakan ba ya nufin gamsuwar da ita ba ne.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana wannan yarjejeniya da aka cimma a gwamnatin shugaba Barrack Obama a matsayin "kurma".

Karkashin wannan yarjejeniya mai cike da rudani, Amurka za karbi ‘yan gudun hijira 1 da 250 da suka nemi mafaka a Australia.

Ita kuwa gwamnatin Australia ta amince ta karbi ‘yan gudun hijira daga Guatemala da Honduras da El Salvador da suka bukaci matsugunni a Amurka.

Akasarin ‘yan gudun hijirar da Australia ta ki karba, sun fito ne daga Iran da Afghanistan da Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.