Bakar fata ya hallaka mutane a Amurka
Jami’an ‘yan sandan Amurka sun tabbatar da mutuwar mutane uku fararen fata bayan wani mutun bakar fata ya bude mu su wuta a birnin Fresno da ke jihar California, harin da ake kallon a matsayin na nuna wariyar launin fata.
Wallafawa ranar:
Jami’an ‘yan sandan sun ce, Kori Ali Muhammad ya bude wuta kan mai uwa da wabi har sau 16 a cikin dakikoki 90.
Majiyar tsaro ta ce, an jiyo mutumin na fadin Allah mai girma a cikin harshen Larabci a yayin kaddamar da farmakin.
Amma jami’an tsaro sun ce, harin ba na ta’addanci ba ne illa kawai na nuna kiyayya ga wani nau’in jama’a.
Tuni dai aka cafke maharin mai shekaru 39 wanda ya bayyana a shafin sada zumunta cewa, ya ki jinin fararen fata.
Ba a karon farko kenan ba da ‘yan bindiga ke bude wuta kan gungun jama’a a Amurka, in da wata kididdiga ke nuna cewa, kimanin mutane dubu 30 na rasa rayukansu ta hanyar irin wannan harin a Amurka a kowacce shekara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu