Isa ga babban shafi
MDD

Namun dawa na dab da karewa a gandayen daji

Kungiyar kare dabbobin dawa a duniya WWF ta yi gargadin cewa kashi 45% na dabbobin da ke cikin kebabbun gandayan daji sama da 200 da ake da su a sassan duniya na fuskantar barazanar karewa sakamakon farautarsu da ake yi ba akan ka’ida ba.

Gandun Dajin Yankari mai yawan Giwaye a yammacin Afrika
Gandun Dajin Yankari mai yawan Giwaye a yammacin Afrika yankarigamereserve.com
Talla

Gwanki, da Giwa da kuma Damusa na daga cikin wadanda suka fi fuskantar wannan barazana sakamakon yadda mafarauta ke kashe namun na dawa.

Manyan gandun daji a kasashen Australia da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo da tsibirin Galapagos na taimakawa wajen kare namun dajin.

Amma rahoton ya bayyana fargaba ga yiyuwar karewar dabbobin a duniya saboda farautarsu da ake yi da kuma saran itace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.