Isa ga babban shafi
Israel-Palestine

An kashe wata dalibar Birtaniya a birnin Kudus

Wani Bafalasdine ya hallaka wata daliba ‘yar asalin Birtaniya bayan ya daba ma ta wuka a kusa a tsohon birnin Kudus, in da dubban Yahudawa da Kiristoci suka taro don gudanar da ibada.

Jami'an tsaron birnin Kudus sun bayyana maharin a matsayin mai tabin hankali
Jami'an tsaron birnin Kudus sun bayyana maharin a matsayin mai tabin hankali REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Jami’an bada agajin gaggawa sun ce, an garzaya da Hannah Bladon mai shekaru 23 kuma daliba a jami’ar Birmingham zuwa asibiti bayan aukuwar lamarin, amma daga bisa ta riga mu gidan gaskiya.

Wani jami’in ‘yan sandan Birnin Kudus, Yoram Halevy ya bayyana maharin mai suna Jamil Tamimi a matsayin mai fama da tabin hankali.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya alakanta kisan da ayyukan ta’addanci.

Majiyar ‘yan sanda ta ce, maharin ya zaro wukar ce daga cikin wata jaka kafin ya daba wa matar a kirjinta.

An dai bayyana Hannah Bladon a matsatyn dalibar Birmingham da ke karatun wani Kwas na hadin gwiwa a Jami’ar Hebrew da ke Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.