Isa ga babban shafi
Syria

Martanin kasashen duniya kan harin Amurka a Syria

Kasashen Rasha da Iran sun yi Allah wadai da hare haren saman da Amurka ta kaddamar a cikin Syria wanda ya hallaka sojojin kasar guda 4.

Kasashen duniya na mayar da martani kan harin da Amurka ta kai Syria a matsayin gargadi.
Kasashen duniya na mayar da martani kan harin da Amurka ta kai Syria a matsayin gargadi. Ferhat Dervisoglu/Dogan
Talla

Kakakin fadar shugaban Rasha Dmitry Peskov, ya ce matakin da Amurka ta dauka zai kara tabarbarewar al’amura ganin irin matsalolin da suka adabi kasar

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Bahram Ghassemi ya ce suna adawa da duk wani shirin kai hari ko daukar matakin soja a Syria.

Ita kuwa Birtaniya tabi sahun Israila da Saudiya ne wajen goyan bayan harin.

Suma ‘yan tawayen Syria sun bukaci ci gaba da kai hare haren.

Kakakin ‘yan Tawayen, Ahmad Ramadan ya ce daukacin ‘yan adawar kasar na yabawa da wannan mataki, kuma suna bukatar ganin an fadada shi.

Tashar talabijin din Syria ta ruwaito cewar harin ya yi mummunar ta’adi, kuma suna daukar matakin a matsayin wani nuna karfi.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yaba da abinda ya kira babban sakon da aka aikewa shugaba Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.