Isa ga babban shafi
Syria

Amurka ta kai harin makami mai linzami Syria

Amurka ta yi gaban kan ta wajen kaddamar da hare hare da makamai masu linzami a tashar jiragen saman Syria bayan harin makami mai guba da aka samu a kasar wanda ya hallaka mutane 86.

Makamin USS Ross a Méditerranée da Amurka ta kai hari da shi Syria
Makamin USS Ross a Méditerranée da Amurka ta kai hari da shi Syria Robert S. Price/Courtesy U.S. Navy/Handout via REUTERS
Talla

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da ke jawabi kan harin, ya ce sun kaddamar da shi ne a matsayin aikewa da wani sako ga shugaba Bashar Al Assad da kuma kare matsayin kasar su.

Trump ya bukaci hadin kan kawayen Amurka wajen daukar matakan da suka dace dan kawo karshen irin wannan kazamin hari da ke ritsawa da fararen hula.

Fadar shugaban ta sanar da cewar an kai hari da makamai masu linzamin har sau 59 a tashar jiragen Shayrat inda Amurka ta ce anyi amfani da shi wajen kai harin ranar talata.

Bayanai sun ce Amurka ta kai harin ne daga jiragen ruwan yakin ta da ake kira USS Ross da USS Porter da ke tekun Baharrum.

Wannan na zuwa ne bayan kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a karo na biyu ya kasa amincewa da shirin gudanar da bincike kan harin makami mai guban da ya kashe mutane 86.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.