Isa ga babban shafi
Rasha-Syria

Kasashen duniya sun caccaki Rasha kan Syria

Manyan kasashen duniya sun caccaki Rasha a zauren Kwmitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bisa harin makami mai guba da ya hallaka mutane fiye da 70 a arewacin Syria.

Mutane 72 sun rasa rayukansu saboda harin makami mai guba da aka kaddamar a Syria
Mutane 72 sun rasa rayukansu saboda harin makami mai guba da aka kaddamar a Syria Reuters
Talla

A zaman tattaunawar da kasashen suka gudanar a wannan Laraba a birnin New York, Rasha ta ce makami mai guba mallakin ‘yan tawayen Syria ne ya hallaka fararen hula, ikirarin da bai samu karbuwa ba.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya da Kwamandan ‘yan tawayen da kuma kwararru kan makamai masu guba duk sun ce, hujjojin da ake da su sun nuna cewa, gwamnatin Syria ce ta kaddamar da farmakin.

Kungiyar da ke sa ido kan hakkin dan Adam a Syria ta ce, kananan yara 20 da kuma manya 52 ne suka mutu a harin wanda aka kai a garin Khan Sheikhoun da ke lardin Idlib.

Zaman taron na yau ya disarar da taron neman tallafa wa Syria da ake gudanarwa a birnin Birussels.

Kimanin masu bada agaji 70 ne ke tattaunawar bada tallafi ga Syria da yaki ya daidaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.