Isa ga babban shafi
EU-Syria

EU ba ta amince wa Assad ya taka rawa a Syria ba

Kasashen Turai sun ce ba su amince a bai wa Bashar al-Assad damar taka rawa dangane da makomar kasar Syria bayan shawo kan rikicin kasar ba.Wannan dai mataki ne da taron ministocin harkokin wajen kasahsen yankin na Turai da aka gudanar a jiya Lititin ya dauka.

Shugaban Syria Bashar al Assad
Shugaban Syria Bashar al Assad REUTERS
Talla

Shugabar Ofishin kare manufofin ketare ta kungiyar Turai Federica Mogherini, wadda ke zantawa da manema labarai a birnin Brussels, ta ce matsayin da suka dauka shi ne Bashar al- Assad ya sauka daga karagar mulki domin kuwa ta hakan ne kawai za a iya kawo karshen rikicin kasar.

Mogherini ta ci gaba da cewa abu ne mai matukar wuya a iya samar da zaman lafiya a Syria matukar dai aka ce Assad zai sake taka wata rawa a fagen siyasar kasar nan gaba.

Shugabar ta Ofishin kare manufofin ketare ta Turai na jagorantar wani taron hadin gwiwa na yini biyu ne da Majalisar Dinkin Duniya kan yadda za a tinkari matsalolin da al’ummar Syria ke fama da su, musamman rashin abinci da muhalli da kuma magunguna.

To sai dai matsayin na kasashen yankin Turai ya yi hannun riga da matsayin Amurka, wadda a makon da ya gabata ta ce, muhimmin abu a wajenta shi ne fada da ta’ddanci amma ba kawo karshen mulkin Assad ba.

Matakin da sabuwar gwamantin Amurka ta dauka dangane da wannan rikici da ya share tsawon sama da shekaru 6, ya yi matukar sanyaya gwiwar masu adawa da shugaba Assad da kuma sauran kasashe da ke mara wa 'yan tawayen kasar baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.