Isa ga babban shafi
Syria

An koma teburin sasanta rikicin Syria a Geneva

An koma zaman tattaunawar sasanta rikicin Syria a Geneva a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, sai dai ana fargabar samun ci gaba saboda yadda gwamnatin kasar da ke samun galaba kan 'yan tawaye a fagen daga ke jan kafa wajen sassauta matsayinta.

An koma teburin sasanta rikicin Syri da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta a birnin Geneva
An koma teburin sasanta rikicin Syri da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta a birnin Geneva REUTERS/Salvatore Di Nolfi/Pool
Talla

Mataimakin Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman Ramzy Ezzeldin Ramzy ya gana da bangarorin gwamnati da kuma 'yan adawa daban daban, in da ya ce yau ake saran fara tattaunawar gadan-gadan.

Yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da bangarorin biyu suka cimma a can baya ta sukurkuce a ‘yan kwanakin nan bayan ‘yan tawayen sun kaddamar da hare-haren ba zata a Damascus da tsakiyar lardin Hama.

Wannan ne ya tirsasa wa dakarun shugaba Bashar al Assad mayar da martani kan ‘yan tawayen.

Yanzu dai an kwashe sama da shekaru 6 ana tashin hankali a Syria wanda ya hallaka mutane sama da dubu 320, yayin da fiye da miliyan 5 suka zama 'yan gudun hijira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.