Isa ga babban shafi
Birtaniya

Khalid Moshood ne ya kai harin London

Rundunar 'yan sandan Birtaniya sun bayyana Khalid Moshood haifaffan kasar a matsayin mutumin da ya kai harin birnin London wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku.

Jami'an 'yan sandan Birtaniya sun kama mutane 8 da ake zargi da hannu a harin birnin London
Jami'an 'yan sandan Birtaniya sun kama mutane 8 da ake zargi da hannu a harin birnin London REUTERS/Darren Staples
Talla

'Yan Sandan sun kuma sanar da kama mutane 8 cikin su har da mata 3 da ake zargi da hannu a harin na ta'addanci.

Minsitar cikin gidan kasar Amber Rudd da Magajin Garin birnin London Sadiq Khan sun shaida wa wani taro da aka gudanar a jiya Alhamis cewar birnin ba zai bada kai bori ya hau ba dangane da hare haren ta’addanci.

Tuni dai kungiyar ISIS ta dauki allhakin kaddamar da farmakin wanda ya yi sanadiyar jikkatar mutane 40 da kuma ke samun kulawa a asibiti.

Shugabannin kasashen duniya sun yi Alla-wadai da wannan harin wanda ke zuwa a dai dai lokacin da nahiyar Turai ke cikin dari-darin ayyukan ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.