Isa ga babban shafi
Libya

Tarayyar Turai na son kulla yarjejeniya da Libya kan ‘Yan ci-rani

Ministocin cikin gidan kasashen Turai da takwarorinsu na arewacin Afrika da ke kan iyaka da tekun Bahrum sun gudanar da taro a birnin Rome domin daukar matakan dakile kwararar ‘yan ci-rani da ke ratsa Libya zuwa Turai.

'Yan ci-rani daga Afrika ke ratsa Libya zuwa Turai
'Yan ci-rani daga Afrika ke ratsa Libya zuwa Turai REUTERS/Jon Nazca
Talla

Tarayyar Turai na son ta kulla yarjejeniya ne da Libya kamar irin wadda ta kulla da Turkiya na takaita kwararar ‘yan gudun hijira.

Taron Ministocin ya kunshi na kasashen Turai guda 8 da kuma kasashen arewacin Afrika da suka kunshi Algeria da Tunisia da kuma Libya wadanda suka yi iyaka da tekun Bahrum.

Manufar taron shi ne rage yawan dimbin ‘yan ci-ranin da ke ratsowa ta Libya zuwa kasashen Turai.

Kuma rahotanni sun ce kasashen Turai na son kulla yarjejeniya da Libya kamar irin wadda suka kulla da Turkiya da ta fuskanci suka daga ‘yan rajin kare hakkin bil’adama.

Libya dai ta nemi taimakon kudi kimanin miliyan 800 na yuro domin samar da kayan tsaron iyakokin ruwanta da suka hada da jirgi mai saukar Angulu da kwale-kwale na zamani domin farautar masu safarar yan ci-rani.

Adadin ‘yan ci ranin da ke ratsa teku daga Libya yawancinsu ‘yan Afrika na dada karuwa inda a 2017 kawai sama da 20,000 suka isa Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.