Isa ga babban shafi
Amurka

CIA na da damar leken asirin jama'a- Wikileaks

Shafin fallasa bayanan sirri na WikiLeaks ya ce, hukumar leken asiri ta Amurka CIA na da damar bibiyar sirrikan miliyoyin mutane ba tare da saninsu ba a duk lokacin da ta so.

Wikileaks ta ce, CIA na da damar tasar bayanan miliyoyin jama'a
Wikileaks ta ce, CIA na da damar tasar bayanan miliyoyin jama'a
Talla

Cikin rahoton da shafin ya wallafa ya ce, CIA za ta iya amfanin da na’urar talabijin a matsayin rikodar bibiyar sirrikan mutane, sai kuma amfani da motocin jama’a wajen satar bayanansu.

Akalla takardun bayanai kan wannan fallasa 9000 ne shafin na Wikileaks ya watsa wanda ya same su daga hukumar binciken sirrin ta Amurka.

Binciken ya nuna cewa hukumar ta CIA na amfani da kura-kurai ko kuma gazawar da ta gano a jikin na’urorin amfani na zamani da aka kera ba tare da bayyana kura-kuran ga kowa ba don amfani da damar wajen leken asirin jama’a.

Kazalika bayanin fallasar shafin na WikiLeaks ya kara da cewa hukumar leken asirin Amurkan ta samar da wasu fasahohin zamani da aka fi sani da Virus a Turance sama da 1000 da ta ke watsawa a shafin Intanet domin samun damar tatsar bayanan sirri daga miliyoyin wayoyin hannu kirar Android da Iphone da kuma talabijin kirar Samsung, sai kuma fasahar Microsoft ta komfuta, wadanda hukumar ta CIA ke iya maida su tamkar abin daukar maganar da za su iya sauraren abin da ake ciki a duk lokacin da suka so.
 

Ko da yake fadar White House ba ta ce komai ba dangane da fallasar mafi girma da aka taba gani a wannan fannin, idan hakan ta tabbata zai zama babban abin kunya ga gwamnatin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.