Isa ga babban shafi
Afrika-Turai-amurka

Yakar Rashawa domin kawar da ta'addanci

Kungiyar Transparency International ta ce akwai bukatar gwamnatocin kasashen yammaci su kara kaimi wajen yakar Rashawa Muddin da gaske suke wajen yakar ayyukan ta’addanci, da suka kunshi ISIL da Boko Haram.

Kungiyar Transparency International
Kungiyar Transparency International
Talla

Rashawa a kasashen Najeriya, Libya da Iraqi a cewar kungiyar na taka rawa wajen yaduwar ayyukan ta’addanci a wadanan kasashe.

A rahoton da ta fitar mai shafuka 44 kungiyar Transaparency Internationale ta ce, rashawa ita ce ginshikin ayyukan ta’addanci da ke ci gaba da yaduwa a kasashe da dama.
Rahotan ya ce tsatsauran ra’ayi ya fito ne daga cikin al’ummar da ake musgunawa a tsarin tafiyar da mulki.
Kungiyar ta kuma bayyana takaicinta kan hare-hare da ake kai wa IS a Iraqi da Syria, wanda ke ruguza tsofin gine-gine.

Transparency ta ce, kungiyoyin jihadi irinsu IS sun bijiro ne sakamakon cire rai daga tsarin mulki da ya kamata ya yi tasiri a rayuwarsu

Kungiyar ta ce ya zama tilas gwamnatocin kasashen yamma su mayar da hankali wajen dawo da da’a da dakile rashawa da mulkin kama karya, muddin ana neman sake dawo da zaman lafiya a kasashen da yaki ya tagayara
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.