Isa ga babban shafi
Amurka

''Amurka ba zata matsawa Isra’ila wajen kafa kasar Falasdinu ba''

Fadar Shugaban kasar Amurka ta ce ba zata matsawa kasar Isra’ila wajen kafa kasar Falasdinu dan kawo karshan rikicin Gabas ta tsakiya ba, a ganawar da shugaba Donald Trump zai yi da Firaminista Benjamin Netanyahu yau laraba a Washington.

shugaban Amurka Donald Trump
shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Jim Bourg
Talla

Wani babban jami’in fadar shugaban Amurka ya ce ba zasu ci gaba da tsoma baki kan gine-gine a Yankunan Falasdinawa ba, sai dai goyan bayan yarjejeniyar da bangarorin biyu suka kulla.

Jami’in ya ce samun kasar Falasdinu da ba zai wanzar da zaman lafiya a Yankin ba, ba abinda zasu goyi baya bane.

Wannan ya tabbatar da sauya matsayin Amurka na ganin Falasdinawa sun samu kasa ta kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.