Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Kyamar Musulunci goyon baya ne ga ta'addanci - Guterres

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, ya ce, nuna kyama ga addinin Islama na rura wutar ta’addanci a sassan duniya.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Guterres ya bayyana haka ne bayan ganawarsa da sarki Salman na Saudiya da kuma ministan cikin gidan kasar Mohammed bin Nayef a birnin Riyadh, a karshen mako.

Kalaman babban magatakardar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres, na zuwa a dai dai lokacin da wasu kasashe ke ci gaba da nuna kyamar karbar baki, musamman wadanda suka fito daga kasashen Musulmi.

Babban magatakardar ya ce, nuna kyama ga Islama, wani goyon bayan ne da kungiyar ISIS ko kuma Da’esh ke samu don cigaba da yada Farfagantarta.

Kungiyar ta ISIS dai ta dauki allhakin kaddamar da munanan hare-haren ta’addanci a Saudiya da kuma nahiyar Turai.

‘Yan siyasar turai da ke kyamar baki, kamar su Marine Le Pen ta Faransa, sun kara samun karbuwa bayan samun matsalar kwararar bakin haure a nahiyar, wadanda akasarinsu sun kauracewa yake-yake ne daga kasashensu na asali kamar Syria da Iraqi.

Mr. Gutetres ya ce, babu yadda za su samu nasara kan yaki da ta’addanci a Syria ba, matukar ba a samar da mafitar siyasa ba ga al’ummar kasar.

Gutteres dai ya isa Saudiya ne daga Turkiya, kuma ana saran isarsa Dubai a yau Litinin don halartar taron gwamnatocin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.