Isa ga babban shafi
Amurka- Yemen

HRW ta bukaci Amurka ta biya diyya a Yemen

Kungiyar Human Right Watch ta bukaci Amurka da ta biya diyya ga iyalan wadanda suka mutu ko suka samu rauni a harin da dakarun kasar suka kai Yemen, in da fararen hula 23 suka gamu da ajalinsu.  

Kananan yara na cikin wadanda harin ya ritsa da su a Yemen kamar yadda masu kare hakkin dan Adam suka ce
Kananan yara na cikin wadanda harin ya ritsa da su a Yemen kamar yadda masu kare hakkin dan Adam suka ce REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Kungiyar Human Right Watch ta bayyana damuwarta kan abin da ta kira sakaci in da, ta bukaci rundunar sojin Amurka da ta gudanar da bincike kan kisan farraren hula  a harin.

Shugaba Donald Trump ne ya bada umarnin kaddamar da harin da nufin tarwatsa tungar mayakan al-Qaeda a Yemen, kuma a karon farko kenan da Amurka ta kai irin wannan farmakin tun bayan darewar Trump a karagar mulki a cikin wannan shekarar.

To sai dai bisa dukkan alamu fararen hula ne suka fi mutuwa a harin kamar yadda masu fafutukar kare hakkin dan Adam suka ce, yayin da Amurka ta ce, sai da aka yi nazari sosai kafin kai farmakin na ranar Asabar.

Shekaru biyu kenan da yaki ya barke a Yemen sakamakon rikici tsakanin bangarorin gwamnati da mayakan Houthis da ke kokarin kifar da gwamnatin shugaba Abdourabuh Mansour Hadi, al’amarin da ya bai wa mayakan al-Qaidan mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.